Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan kudaden N-Power

121

Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan kudaden da ba a biya ba, na masu cin gajiyar shirin Npower wadanda suka gama.

Tace an samu amincewa domin biyan kudaden da ba a biya ba ga wadanda suka bar shirin Npower a rukunonin A da B.

Ministar harkokin jin kai, kula da annoba da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouq, tace an mika amincewar biyan kudaden har na watan Yunin da ya gabata, zuwa ofishin babban akawu na kasa, domin biyan kudaden.

Tace amincewar biyan kudaden da ake bi wanda ba a aika zuwa ga ofishin babban akawu ba, ita ce ta watan Yulin da ya gabata, domin yan rukunin B.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × one =