Yan Majalisa za suyi kamun kafa ga gwamnonin domin Buhari ya sake bude makarantu

43

Majalisar Wakilai ta gana da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi akan hanyoyin da za abi a sake bude makarantu domin bawa dalibai damar zana jarabawar kammala babbar sakandire ta WAEC.

Kwamitin ilimin bai daya na majalisar ya gudanar da zaman tattaunawa tare da ma’aikatar ilimi ta tarayya da hukumar jarabawar WAEC a Najeriya domin tattauna matsalar.

Majalisar ta yanke shawarar ganawa da kungiyar gwamnonin Najeriya wadanda ake sa ran zasu yi kamun kafa domin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin sake bude makarantu.

Masu ruwa da tsaki a wajen ganawar sun amince cewa muddin ana san cimma ranar fara rubuta jarabawar ta WAEC a watan Satumba, akwai bukatar shugaba Buhari da kungiyar gwamnoni su shigo ciki wajen samar da matsaya mai kyau akan lokaci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen + thirteen =