Yan Israila na zanga-zangar kin jinin Fira Minista Netanyahu

80

Dubban ‘yan Israi’la sun gudanar da zanga-zanga a Tel Aviv, don nuna adawa da abin da suka kira kangin tattalin arziki da salon gwamnati na yaki da annobar korona ya tsunduma al’umma ciki.

Matasa da dama sun cika makil a dandalin taro na Robin Square sanye da takunkumai, sai dai ba tare da bawa juna tazara ba.

A birnin Kudus kuwa daruruwan mutane sun taru a kofar gidan Fira minista Benjamin Netanyahu, suna kiran ya sauka daga kan karagar mulki.

‘Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi, domin tarwatsa dubban masu zanga-zangar, abin da ya rikide ya koma tashin hankali.

Masu zanga-zangar na kuma nuna damuwa kan yadda diyyar da gwamnati ke bayarwa ba ta isa gare su a kan lokaci.

Mutane da dama a kasar sun tagayyara, kuma suna nuna takaici a kan yadda dokokin da aka kafa na yaki da cutar ta korona a kasar ke ci gaba da janyo musu wahalhalu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 − six =