Wani rahoto ya zargi Magu da sace kudin ruwa akan naira biliyan 550

22

Wani kwamitin shugaban kasa da ya binciki yadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC take kula da kudaden satar da aka kwato, ya zargi mukaddashin shugaban hukumar, Ibrahim Magu, da laifi.

An kama Ibrahim Magu ranar Talata kuma har yanzu kwamitin karkashin jagorancin mai shari’ah Ayo Salami na cigaba da tuhumarsa dangane da zarge-zargen badakala da rashin gaskiya wajen kula da kadarorin satar da hukumar ta kwato.

A jawabinsa na farko ga jama’a dangane da batun Magun, shugaban kasa Muhammadu Buhari yace akwai zarge-zargen almundahana sosai akan shugaban na EFCC, kuma gwamnatinsa ta dauki mataki bayan da ta bibiyi zarge-zargen a karon farko.

La’akari da rahoton kwamitin shugaban kasa na binciken kadarorin satar da aka kwato wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa a shekarar 2017, kamfanin dillancin labarai na kasa ya sanar da yadda akai zargin an sace kudaden ruwan da suka taru akan kudi naira biliyan 550 da hukumar EFCC ta kwato.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 6 =