Kasar Sudan ta ayyana dokar ta baci a yankin yammacin kasar na Darfur.
Matakin ya biyo bayan karuwar rikice-rikice tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro, bayan makonni ana zanga-zanga.
Kungiyar tarayyar Afrika da ofishin majalisar dinkin duniya a Darfur sunce sun aika da wata tawaga zuwa garin Kutum, biyo bayan samun rahoton kone ofishin yansanda da motoci.
A ranar Lahadi, jami’an tsaro suka harba harsasan bindiga domin tarwatsa wata zanga-zangar, inda aka bayar da rahoton kisan mutane 5.
An jima ana gudanar da zanga-zangar lumana a bangarori da dama na yankin, inda masu zanga-zangar ke neman korar gurbatattun ma’aikata daga aiki tare da janye sojoji dauke daga makamai daga garuruwa da kauyuka.
Fira-Ministan Sudan, Abdalla Hamdok, a ranar Lahadi yayi alkawarin kawo karshen tabarbarewar tsaro.