Shugaba Buhari ya nada sakataren zartawa ga hukumar aikin hajjin kiristoci

27

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Yakubu Pam a matsayin zababben sakataren hukumar aikin hajjin kiristoci.

Kafin nadinsa, Yakubu Pam wanda reverend pastor ne, shine shugaban hukumar aikin hajjin kiristoci ta jihar Filato.

An haife shi a ranar 20 ga watan Fabrairun 1960 a Gyel dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato, Yakubu Pam yana da digiri akan ilimin kiristanci.

A matsayinsa na babban limamin coci, Yakubu Pam ya karbi mukamin da gogewar shugabancin kiristanci na tsawon shekaru 30, hade da kyakykyawar fahimtar dabbaka zaman lafiya da sasanta rikice-rikice a yankunan Arewacin kasarnan.

Limamin kiristan ya rike mukamai dayawa a tsarin addinin kirista, cikinsu har da shugaban kungiyar kiristocin arewacin Najeriya, daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 + 8 =