Sashen daukar sojoji aiki da tsugunnarwa ya musanta labaran karya da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa sashen ya fitar da takardun neman shiga aikin soji.
Jami’in daukar sojoji aiki na jihar Jigawa, Manjo A.Y. Abdulmalik ya musanta daukar aikin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse.
Yace wasu batagarin mutane suna fitar da takardun neman shiga aikin soji na karya a shafin sadarwa na zamani da suka bude domin karbar kudade a hannun jama’a.
Manjo Abdulmalik ya kara da cewa takardun neman aikin soja dake yawo ba na gaskiya bane kuma basu da wata alaka da daukar aikin soji.
Yace har yanzu sashen daukar sojoji aiki bai bude shafin daukar sabbin sojoji ba, dan haka ya bukaci al’umma dasu rinka samun sahihan bayanai a hakikanin shafin yanar gizon hukumar soji ta kasa.