A wajen taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi a jiya, an amince da fitar da kudin da za a biya kamfanin Siemens domin aikin wutar lantarki.
Majalisar ta amince a saki Naira biliyan shida da miliyan dari tara da arba’in wadanda za a kai waje, da Naira biliyan daya da miliyan dari bakwai da goma a cikin kasa, a matsayin kason Najeriya a yarjejeniyar da aka shiga da kamfanin Siemens na Jamus a shekarar 2019.
Majalisar zartarwar ta kuma amince da yarjejeniyar sufurin jiragen sama tsakanin Najeriya da Amurka, a wajen taron majalisar wanda aka yi ta bidiyo, karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, ta shaidawa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa ita da ministan wuta, Saleh Mamman sun kawo maganar wajen taron majalisar zartarwa.
A watan Yulin bara, gwamnatin tarayya tare da kamfanin Siemens suka sanya hannu kan takardar yarjejeniya dangane da shirin gyara wutar lantarki a Najeriya.