Gwamnatin Tarayya ta warewa yan siyasa kashi 10 cikin 100 na mutane 774,000 da za a dauka aiki

74

Gwamnatin tarayya ta warewa yan siyasa kashi goma cikin dari na ma’aikata dubu dari bakwai da saba’in da hudu da za a dauka wani aikin gwamnati na musamman, a cewar kakakin kwamitin zaben ma’aikatan na jihar Kano, Abubakar Muhammad Janaral yayin zantawa da manema labarai.

Yace jihar ta raba takardun cikewa guda dubu hudu da dari hudu ga yan siyasa daga cikin guraben aiki dubu arba’in da hudu na ‘yan jihar.

Muhammad Janaral yace an warewa yan siyasa guraben ne domin a kaucewa sa hannunsu a hanyoyin zaben ma’aikatan.

Ya kara da cewa kwamitin zaben na jihar Kano ya kafa kananan kwamitoci a kananan hukumomi wadanda suka hada da masu rike da sarautun gargajiya da malaman addini da kungiyoyin fararen hula domin duba aikin zaben.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven + seven =