Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun NECO da NABTEB

71

Gwamnatin tarayya ta saki cikakken jadawalin jarabawowi domin yan ajin karshe. Za a gudanar da jarabawowin daga ranar 17 ga watan Augusta zuwa 18 ga watan Nuwamba.

Jarabawowin sun hada da jarabawar kammala babba sakandire wacce hukumar jarabawa ta kasa NECO ke shiryawa, wacce za a fara daga ranar 5 ga watan Oktoba kuma a kare a ranar 18 ga watan Nuwamba.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajuiba, ya sanar da haka a jiya a Abuja, bayan an gudanar da zaman ganawa daban-daban tare da shugabannin hukumomin jarabawowin na kasarnan.

Gwamnati ta kuma ce za a fara zana jarabawar WAEC a ranar 17 ga watan Augusta.

Ministan na ilimi yace za a fara jarabawar NABTEB a ranar 21 ga watan Satumba, a kare a ranar 15 ga watan Oktoba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 2 =