Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Biliyan 15.8 domin biyan alawus-alawus na hadari

29

Gwamnatin tarayya tace kawo yanzu ta kashe naira biliyan goma sha biyar da miliyan dari takwas domin biyan alawus-alawus na hadari a asibitocinta na koyarwa da cibiyoyin lafiya a fadin kasarnan.

Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, ya sanar da haka a Abuja lokacin da yake jawabi ga manema labarai a wajen wani taron ganawa tare da shugabannin kungiyar likitocin dake neman kwarewa.

An gudanar da taron ganawar domin duba matakin da ake kai na aikwatar da yarjejeniyar da bangarorin biyu suka shiga, domin dakile barazanar komawa yajin aikin da likitocin suka yi.

Chris Ngige ya cigaba da cewa har yanzu ba a biya alawus na watan Yuni ba, kasancewar wasu sabbin abubuwa sun shafi kasafin kudi, abubuwan sune biyan manyan likitoci da masu koyon aiki da masu yiwa kasa hidima da kuma yan sa kai.

Sai dai, ya kara da cewa tuni gwamnati ta fara aiki tare da kwamitin karta kwana na shugaban kasa domin lalubo bakin zaren matsalar, musamman ta yan sa kai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one + eleven =