An kashe akalla fararen hula tara a wani sabon hari da wasu mayaka suka kai a lardin Cabo Delagado mai fama da rikici a arewacin kasar Mozambique, a cewar wasu majiyoyin cikin gida.
Hare-haren da aka kai a gundumomin Cabo Delgado a ranar Laraba, sun tilastawa mutune arcewa daga gidajen su, inda suka yi mafaka a waje wuri itatuwa dake kusa.
Wata kungiyar ‘yan bindiga sun kai sumame a kauyen Tandacua a Macomia, suna neman abinci a cewar mazauna wurin.
Maharan sun isa wurin ne da misalin karfe shida na yamma, agogon kasar, ‘yan kauyen da dama sun arce daga kauyen a cewar wani mazauni kauyen daya nemi a sakaya sunan sa.
Kungiyar ‘yan bindiga ta al-Shabab ce ta kai wadannan hare-haren a Arewacin kasar Mozambique.