
Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya gargadi dukkan wadanda ya nada mukamai da su kyautata alaka da majalisun kasa.
A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan yada labarai, Garba Shehu ya fitar ta ambato Shugaba Buhari na cewa ba zai lamunci duk wani rashin biyayya ga majalisa daga duk wani jami’in bangaren zartarwa ba.
Ta ce shugaban ya yi wannan jan kunne ne lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar dattawa; Ahmad Lawan, da kakakin majalisar wakilai; Femi Gbajabiamila, inda suka tattauna game da wasu ayyukan baya-bayan nan na majalisa, a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan dambarwar da ta sanya majalisar dakatar da wani shirin daukar mutane dubu dari bakwai da saba’in da hudu aikin wucin gadi, sakamakon takaddama da ministan kwadago.
Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani a kan ko gargadin na Buhari na nufin minista Festus Keyamo zai ba da kai ga bukatar majalisar ba, game da batun daukar dubban matasan aikin.