Buhari ya sanya sunan Goodluck a tashar jirgin kasa

49

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya sunan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a tashar jirgin kasa dake garin Agbor a jihar Delta.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya sanar da haka lokacin da yake duba aikin titin jirgin kasa daga Warri zuwa Itakpe.

Ministan ya kuma bayyana gamsuwarsa akan ingancin aikin a tashoshi daban-daban, inda yace an kammala aikin titin jirgin kasa na Warri zuwa Itakpe kuma ana shirin kaddamarwa.

Tashar jirgin kasan dake Agbor ita ce cibiyar titin jirgin kasan na Warri zuwa Itakpe. Ta kuma hade da titin jirgin kasa na Benin zuwa Onitsa, da sauran bangarorin kasarnan.

Dangane da dawowa jigila akan titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna, Rotimi Amaechi yace akwai bukatar ake bawa juna tazara tare da tabbatar da cewa ba a yadawa fasinjoji cutar corona ba.

Yayi bayanin cewa kimanin fasinjoji dubu 4 ne suke tafiya akan titin jirgin kasan na Abuja zuwa Kaduna a kowace rana, a saboda akwai bukatar a dauki matakan kariya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 4 =