Karancin wutar lantarki a Najeriya yana jawo asarar kudade masu dumbin yawa, kiyasin naira triliyan 10 da biliyan 100 kowace shekara, a cewar bankin duniya.
A wani sabon rahoto, bankin na duniya yayi nuni da cewa sauyin da aka samu daga gwamnati zuwa hannun yan kasuwa, wanda aka fara a shekarar 2013, bai haifar da da mai ido ba.
Rahoton yace hakan ya jawo rashin yarda tsakanin manyan masu ruwa da tsaki da jama’ar kasa a bangare inganta wutar lantarki.
Rahoton yace sauye-sauye masu nagarta na bukatar bin hanyoyin da suka kamata wajen shawo kan matsalolin da ake fuskanta, tare da assasa shirin dorewar tattalin arziki daga gwamnatin tarayya domin tabbatar da samar da isassun kudade wajen cike gibin da ake samu na kudaden wuta, da sauran matakai.
Bankin na duniya ya bayyana bangaren wutar lantarki, musamman bangaren rarrabawa, a matsayin wanda ya gaza kuma yake janyo dumbin asarar kudade.