
Kasa da mako guda bayan wasu mutane sun rusa wani gini a harabar ofishin jakadancin Najeriya dake Accra a Ghana, wasu tsegaru sun kai hari kan ofishin jakadancin Najeriya dake Jakarta, babban birnin Indonesia.
An gano cewa wadanda suka kai harin ‘yan Najeriya ne dake zanga-zangar zargin nuna musu wariya da take musu hakkin bil’adama daga jami’an hukumar shige da fice na Indonesiya.
A wasu faye-fayen bidiyo da aka dora a yanar gizo, an ga masu zanga-zangar dauke da alluna suna rera wakokin cewa gwamnatin Najeriya bata taimakonsu a kasar.
An ga wasu daga cikinsu sun lalata wata farar mota kirar bus a harabar ofishin, yayin da wasu suka fasa tagogi da kofofin ginin.
Masu zanga-zangar sun kuma jefo tutar Najeriya inda suka yayyaga ta bayan sun ja ta a kasa na wasu mintuna.
Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, yayi Allah wa dai da harin.