Kotu ta haramtawa Obaseki tsayawa takara a zaben cikin gida na PDP

39

Wata babbar kotun tarayya dake zama a Fatakwal jihar Rivers ta haramtawa Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo daga shiga zaben cikin gida na dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP wanda aka shirya yi ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni.

Kamar yadda yazo a takardun kotun, wadanda aka rabawa manema labarai, daya daga cikin yan takarar jam’iyyar ta PDP, Omoregie Ogbeida-Ihama, wanda ya sha alwashin cewa bazai janyewa Obaseki ba, shine ya shigar da karar.

Ogbeida-Ihama ya bukaci kotun da ta haramtawa Obaseki shiga zaben cikin gidan saboda dalilai da dama.

Babban dalilin Ogbeida-Ihama shine kwanannan Obaseki ya shiga jam’iyyar, kuma wadanda suka sayi takardar shiga takara cikin kwanakin da aka kayyade ne kadai za a bawa damar shiga zaben cikin gidan.

Ya kuma kalubalanci sahihancin takardun karatun Obaseki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × one =