Gwamnatin Tarayya tayi hasashen bude makarantu bayan dokar hana tafiya tsakanin jihoshi

42

Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba, ya yi tsokacin cewa za a iya sake bude makarantu a kasarnan bayan an dage dokar hana tafiye-tafiya tsakanin jihoshi.

Ministan ya bayyana haka lokacin taron manema labarai na kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona wanda aka gudanar jiya Litinin a Abuja.

Da yake tabbatar a cewa gwamnati bata sanar da ranar sake bude makarantu ba, yace ma’aikatar baza ta jagoranci ‘yan Najeriya zuwa fadawa hadari ba.

A watan Maris gwamnatin tarayya ta rufe dukkan makarantu a kasarnan, a wani bangare na matakan dakile bazuwar annobar corona.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × two =