Gwamnatin Tarayya ta dage ranar dawo da jigilar jiragen sama

52

Gwamnatin tarayya ta kara wa’adin ranar dawo da jigilar jiragen sama a cikin kasa.

Darakta Janar na hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya, Captain Musa Nuhu, ya sanar da haka jiya Alhamis a wajen taron manema labarai na kwamitin shugaban kasa kan cutar corona, wanda ake gudanarwa kowace rana.

Musa Nuhu yace ranar 21 ga watan Yunin da muke ciki da aka ware domin dawo da jigilar jiragen, ba za ta samu ba.

Najeriya ta rufe filayen jiragen samanta a watan Maris, in banda jigilolin da suka zama tilas, lokacin da kasar ke kokarin magance bazuwar cutar corona, wacce ta jawo mutuwar sama da mutane 400 a kasar.

Gwamnatin a farkon watan da muke ciki tace za a dawo da wasu daga cikin jigilolin jiragen sama a ranar 21 ga watan, ranar da yanzu aka daga.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 + 11 =