Gwamnatin tarayya ta amince da abinda ta kira sake bude makarantu ba tare da matsala ba, a zango na gaba na sassauta dokokin kulle sannu a hankali, wadanda aka sanya da nufin dakile cigaban bazuwar cutar corona.
Sai dai, dalibai ‘yan aji 6 a firamare, da yan aji 3 a karamar sakandire da yan aji 3 a babbar sakandire ne kadai zasu koma makaranta.
Manyan makarantun gaba da sakandire da sauran azuzuwa a makarantun firamare da sakandire, in banda ‘yan azuzuwan karshe, za su cigaba da zama a kulle.
Gwamnati ta kuma dage dokar hana tafiye-tafiye tsakankanin jihoshi, wacce zata fara aiki daga gobe Laraba, muddin za a aiwatar da tafiyar cikin awannin da ba a hana fita ba.
Shugaban kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona, Boss Mustapha, ya sanar da haka a wajen taron manema labarai na kwamitin a Abuja.