gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin kammala dukkan ayyukan titunan da ake yi

63

Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin kammala dukkan ayyukan titunan da ake yi a fadin kasarnan cikin lokacin da aka tsara.

Karamin ministan ayyuka da gidaje, Engineer Abubakar D. Aliyu ya bayar da tabbacin lokacin da yake duba aikin raba titin Abuja zuwa Abaji zuwa Lokoja.

Kamfanin Dantata and Sawoe ne yake gudanar da aikin wanda ya cimma kashi 96 cikin 100 da kammaluwa.

Ministan ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatarsa ta tabbatar da kammala dukkan ayyukan da suka kai kashi 80 zuwa 90 cikin 100 da kammaluwa, inda ya kara da cewa da shi da babban ministan ma’aikatar, Babatunde Fashola, za suyi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da hakan.

Shugaban kamfanin Dantata and Sawoe, Engineer Nasir Dantata, ya bayyana cewa an samu karin hanya a gefen titin, inda ya kara da cewa nan bada dadewa za a kammala aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − twelve =