Gwamnatin Tarayya ta alakanta rabin mace-macen Kano da Corona

44

Gwamnatin tarayya tace jumillar mutane 979 suka mutu sanadiyyar cututtukan da ba a saba gani ba a jihar Kano, cikin makonni 5.

Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya sanar da hakan lokacin taron manema labarai na kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona wanda aka gudanar jiya Litinin a Abuja.

Yace binciken da wata tawagar kwararru da aka tura jihar ta gudanar, ya bayyana cewa kashi 50 zuwa 60 cikin dari na mace-macen da aka yi suna da alaka da cutar corona.

Ehanire ya bayyana cewa mafi yawa daga cikin wadanda suka mutu sun haura shekaru 65 a duniya.

Yace binciken mace-mace ya gano cewa kimanin kashi 65 cikin 100 na mace-macen sun auku a gida, yayin da kashi 38 cikin 100 suka auku a asibiti.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 12 =