An kashe mutane uku bayan wani mutum ya yayyanki mutane da wuka a Ingila

103

‘Yansanda sun tabbatar da cewa mutane 3 sun mutu kuma karin wasu 3 sun samu munanan raunuka bayan an yanyankesu da wuka a wani wajen taruwar jama’a a birnin Reading na Ingila.

An kama wani mutum mai shekaru 25 a duniya daga birnin na Reading, bisa zargin kisan kai bayan an cafke shi a wajen da lamarin ya auku.

Harin ya auku a wani lambu, inda aka soki mutane da dama da wuka.

A yanzu ‘yansanda basa duban lamarin a matsayin mai alaka da ta’addanci, amma an kira jami’an yaki da ta’addanci zuwa wajen.

Majiyoyin tsaro sun shaidawa BBC cewa an kama wani mutum a wajen da abin ya auku, kuma ana kyautata zaton cewa dan kasar Libya ne.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − five =