Yawan Wadanda Suka Kamu Da Corona a Najeriya Sun Karu Zuwa 6,667

29

Alkaluman yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar corona a Najeriya sun karu zuwa 6,667 jiya Laraba, bayan hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da sabbin mutane 284 da suka kamu da cutar.

Kazalika, yawan wadanda kwayar cutar ta kashe sun kai 200, bayan an tabbatar da mutuwar mutane 8 sanadiyyar cutar jiya Laraba.

Hukumar a wani sakon Tuwita data saki jiya Laraba da dare, tace an samu sabbin mutane 284 da suka kamu a jihoshi 13.

A jihar Lagos an samu mutane 1,999, inda jihar Ribas ta biyo baya da mutane 26, yayin da jihar Oyo ke da mutane 19, jihar Borno da Babban Birnin Tarayya na da mutane 8-8, sai mutane 7 a Filato, 6 a Jigawa, 5 a Kano, 2 a Abia, yayin da jihoshin Ekiti da Delta da Kwara da Taraba suke da mutane 1-1.

An samu kari kadan a yawan wadanda suka kamu jiya Laraba, idan aka yi la’akari da yawan wadanda suka kamu shekarajiya Talata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × one =