Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da tsige Farfesa Charles Uwakwe a matsayin shugaban hukumar shirya jarabawa ta kasa, NECO.
Shugaban kasar ya kuma kori mambobi 4 na majalisar gudanarwar hukumar bisa laifuka daban-daban masu alaka da badakalar kudade.
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Charles Uwakwe tun a watan Mayun 2018 bisa zargin sama da fadi da kudade tare da cin amanar aiki. Inda aka nada Abubakar Gana a matsayin shugaban riko na hukumar.
Ana zargin Charles Uwakwe tare da wasu manyan jami’ai da laifin bayar da kwangiloli a majalisar wadanda kudinsu ya kai Naira Biliyan 25, ba bisa ka’ida ba.