Hukumar Lafiya Ta Duniya Da Dakatar Da Gwajin Magani Chloroquine Domin Corona

31

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tace an dakatar da gwajin maganin zazzabin cizon sauro chloroquine a matsayin maganin da zai iya magance cutar corona saboda fargabar samun matsala.

An dakatar da gwajin maganin a kasashe dayawa tsawon wani lokaci, domin kare kai.

Hakan yazo bayan wani binciken lafiya na baya-bayan nan yayi hasashen cewa maganin zai iya kara yiwuwar mutuwar masu fama da cutar corona.

Shugaban Amurka Donald Trump ya tallata maganin na zazzabin cizon sauro, duk da gargadin ma’aikatan lafiya cewa zai iya jawo cututtukan zuciya ga masu fama da cutar corona. Trump ya kuma ce shi da kansa yana shan maganin domin korar kwayar cutar, amma shekaranjiya Lahadi yace ya dena shan maganin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + 10 =