Gwamnoni Za Su Gana Akan Yancin Cin Gashin Kan Bangaren Shari’ah Da Majalisun Dokokin Jihoshi

47

Kungiyar gwamnonin Najeriya a yau zata gana domin tattauna batun cin gashin kai na kudade ga bangaren shari’ah na jihoshi da majalisun dokokin jihoshi.

A wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulrazaq Bello Barkindo, ya fitar a Abuja, tayi nuni da cewa tattaunawar zata zama ta 9 a jerin ganawa ta bidiyon kai tsaye wanda gwamnonin suka yi tun bayan fara dokar kulle sanadiyyar barkewar cutar corona.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Juma’ar da ta gabata, ya sanya hannu akan dokar majalisar zartarwa wacce ta bayar da ‘yancin cin gashin kai na kudade ga bangaren shari’ah na jihoshi da majalisun dokokin jihoshi 36 na kasarnan.

Dokar ta kuma bayar da dama ga Babban Akawu na tarayya da ya cire kudi daga tushe, adadin da ya kamata a bawa bangaren shari’ah da majalisun dokoki, daga kason wata-wata na kowace jiha, domin jihoshin da suka ki bayar da wannan yancin cin gashin kan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 4 =