Gwamnatin Tarayya Zata Fara Shirin Ciyar Da ‘Yan Makaranta A Jihoshi 4 Mako Mai Zuwa

39

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za a fara shirin ciyar da yara ‘yan makarantar firamare mako mai zuwa a jihoshi 4.

A wani bangare na rage radadin illar cutar corona da dokar kulle ga marasa galihu, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a lokacin jawabinsa na farko a watan Maris, ya umarci ma’aikatar jin kai, kula da annoba da walwalar jama’a, da ta yi aiki tare da gwamnatocin jihoshi wajen tsara yadda za a cigaba da shirin ciyar da ‘yan makaranta, duk da an rufe makarantun.

Da take bayar da bayani akan cigaban da aka samu a shirin, ministar jin kai, kula da annoba da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouq, tace za a fara shirin a jihoshin Lagos da Ogun da Kano da Babban Birnin Tarayya, sati mai zuwa.

Ministar a wani jawabinta na baya, tayi tsokacin cewa za a raba abincin gida gida ta hanyar amfani da kati.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 + 5 =