Gwamnatin Jihar Kano Ta Tusa Keyar Almajirai 83 Zuwa Jihar Kebbi

105

Gwamnatin jihar Kebbi ta karbi Almajirai 83 wadanda gwamnatin jihar Kano ta koro zuwa jihar.

Shugaban kwamitin karta kwana kan cutar corona a jihar, Alhaji Jafar Mohammed ne ya karbi almajiran, wadanda ke cikin koshin lafiya, a madadin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu.

Jafar Mohammed ya bayyana cewa yaran sun fito daga kananan hukumomi 7 na Birnin Kebbi, da Kalgo, da Dandi, da Argungu, da Maiyama, da Jega da kuma Yauri, yayin da daya daga cikinsu dan asalin jamhuriyar Nijar ne dake makotaka da jihar.

Yace za a mika dukkan yaran ga shugabannin kananan hukumomin da suka fito, wadanda suka halarci wajen, yayin da za a kai dan Nijar din zuwa kasarsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × five =