Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yayi gargadin cewa iyayen da suka shigar da ‘ya’yansu zuwa makarantun Almajiranci, zasu fuskanci shari’a da daurin shekaru 2 a gidan yari.
El-Rufai ya sanar da hakan lokacin da ya ziyarci wasu Almajirai 200 da aka kwaso daga jihar Nasarawa kuma aka kula da su da tantance su a Kaduna.
Gwamnan ya kuma ce duk wani malamin addinin musuluncin da ya shigar da wani yaro tsarin Almajiranta zasu gurfanar da shi a gaban shari’a tare da daure shi, da kuma cin shi tarar kudi naira dubu 100 zuwa dubu 200 akan kowane yaro guda.
Yace dukkan Almajiran da aka kwaso daga wasu jihoshin kasarnan zuwa jihar, ‘yan asalin jihar Kaduna ne, inda ya kara da cewa gwamnati zata basu dukkan damarmakin da suka cancancesu domin su girma su cigaba.