Buhari Ya Bukaci Kwamitin Karta Kwana Na Shugaban Kasa Kan Corona Da Yayi Aiki Kafada Da Kafada Da Gwamnonin Jihoshi

19

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kiran da a kara samun hadin kai tsakanin gwamnonin jihoshi da kwamitin shugaban kasa na karta kwana kan cutar corona.

Shugaban kasar ya sanar da hakan lokacin da yake ganawa ta bidiyon kai tsaye tare da wasu daga cikin gwamnonin Najeriya jiya Litinin.

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar, yace kwamitin karta kwanan yayi masa bayani akan matakan da za a dauka a gaba, wajen magance annobar a kasarnan.

Yace a dalilin haka shugaban kasar ya umarci kwamitin karta kwanan da yayi aiki tare da gwamnonin wajen ilimintar da mutane tare da daukar matakan da suka kamata wajen kare kai. Daga cikin wadanda suka halarci zauren majalisar zartarwa inda shugaban kasar ya gana ta bidiyon kai tsaye sun hada da ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, da gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele, da shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Ibrahim Gambari, da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × two =