Bankin Access Ya Musanta Korar Ma’aikata Da Rufe Rassa

55

Bankin Access ya musanta rahotannin dake cewa yana shirin korar kashi 75 cikin 100 na ma’aikatansa, tare da rufe rassan bankin sama da 300.

Bankin a wata sanarwa da aka fitar dauke da sa hannun sakatarensa, Mista Sunday Ekwochi, ya bayyana labarin da kanzon kurege wanda aka yada da nufin kautar da hankalin mutane akan kokarin da bankin ke yi na kare ma’aikatansa tare da taimakawa wajen magance asarar ayyukan yi a halin da ake na matsin tattalin arziki.

Sanarwar tace rufe reshen kowane banki, mataki ne da yake bukatar amincewar babban bankin kasa CBN.

A cewar bankin, bai nema ba kuma bai samu amincewar rufe rassan bankin ba, daga babban bankin kasa, kamar yadda ake ta yayatawa.

Ta yi nuni da cewa sanadiyyar annobar corona, ba duka rassan bankin bane za su zama a bude gabadaya ba, har zuwa nan gaba cikin shekararnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × five =