Alkalin da ya sanar da soke zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni, shekarar 1993, mai shari’ah Dahiru Saleh, ya rasu, yana da shekaru 81 a duniya.
Zaben na ranar 12 ga watan Yunin 1993, ana kyautata zaton marigayi MKO Abiola na tsohuwar jam’iyyar SDP ne ya lashe, bayan ya doke makusancinsa a yawan kuri’u, Alhaji Bashir Tofa, na jam’iyyar NRC.
Sanarwar soken zaben wacce ta girgiza kasarnan a ranar 23 ga watan Yuni na shekarar, ta samu sahalewar shugaban kasa na mulkin soja a lokacin, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
An samu labarin cewa tsohon alkalin, ya rasu jiya Alhamis a garinsu Azare, helkwatar karamar hukumar Katagum, ta jihar Bauchi.
An binne shi a fadar sarkin Katagum, a ranar, bisa koyarwar addinin Islama.