Yawan Mutanen Da Suka Kamu Da COVID-19 Jiya Alhamis Ya Karu Zuwa 288

22

Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 jiya Alhamis ya karu zuwa 288 daga 276 da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar shekaranjiya Laraba.

A cewar sabbin alkaluman da cibiyar ta NCDC ta saki, an samu sabbin mutane 14 da suka kamu a jihoshin Lagos da Delta. Jihar Lagos tana da mutane 13, yayin da jihar Delta ke da mutum guda.

Kawo yanzu, mutane 288 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, inda aka sallami mutane 51 daga asibiti bayan sun warke daga cutar, yayin da cutar ta hallaka mutane 7 a Najeriya.

Kididdigar alkaluman yawan wadanda suka kamu a kasarnan ya nuna cewa har yanzu jihar Lagos ce inda cutar tafi kamari a kasarnan.

A Jihar ta Lagos an samu mutane 158 da suka kamu, sai mutane 54 a Babban Birnin Tarayya, sai jihar Osun mai mutane 20, Edo 12, Oyo 11, Bauchi 6, Jihoshin Akwa Ibom da Kaduna suna da mutane 5 kowannensu, Ogun 4, inda jihoshin Enugu, Ekiti, Rivers, Delta da Kwara suke da bibiyu kowanne, yayin da jihoshin Ondo da Katsina suke da dai-dai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − 3 =