Sama da mutane dubu 900 ne aka tabbatar sun kamu da coronavirus a hukumance a fadin duniya, tun bayar barkewar annobar a China, karshen shekarar data gabata, a cewar alkaluman kamfanin dillancin labarai na AFP ta hanyar amfani da majiyoyin hukumomi, wanda aka saki jiya Laraba.
Akalla mutane 905,589 aka ce sun kamu da cutar, cikinsu har da mutane 45,719 da cutar ta hallaka a kasashe 187 a fadin duniya. Mutane 203,608 suka kamu da cutar a Amurka, inda mutane 4,476 suka mutu sanadiyyar cutar.
An samu mutane 110,574 da suka kamu da cutar a Italiya, inda ake da mafiya yawan wadanda cutar ta kashe da mutane 13,155. Sifaniya na da mutane 102,136 da suka kamu da cutar, cikinsu mutane 9,053 sun rigamu gidan gaskiya, yayin da China ke da mutane 81,554 da suka kamu da cutar, wacce ta hallaka mutane 3,312 a kasar.