Ana cigaba da samun karuwar mace-macen da ba a saba gani ba a jihar Kano, bayan an tabbatar da mutuwar wasu mashahuran mutane 12 a jiya Asabar.
Mamatan sun hada da farfesoshi da editan jarida da sauran kwararru.
An binne su a makabartu daban-daban a ciki da wajen kwaryar birnin Kano.
Cikin kwanaki 8 na dokar kulle da suka gabata a jihar, akalla mutane 200 suka mutu sanadiyyar wata cuta da ba bayyana ba.
Shaidun gani da ido da masu aiki a makabartu a jihar sunce mutane dayawa sun mutu kuma a binne su a ‘yan kwanakin nan.
Karuwar mace-macen mutanen na cigaba da haifar da fargaba tare da rudani tsakankanin mazauna jihar.