Shugaba Buhari Ya Roki ‘Yan Najeriya Da Su Kiyaye Bin Dokar Zama A Gida

25

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki ‘yan Najeriya da su kiyaye bin dokar zama a gida, a cewar wata sanarwar da aka fitar daga ofishinsa.

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, yayi nuni da cewa shugaban kasa ya bayar da umarnin sakin tan dubu 70 na hatsi domin karawa akan tallafin da ake bawa ‘yan Najeriya marasa karfi.

Garba Shehu yace za a saki hatsin daga rumbun adana hatsi na kasa.

Daga nan ya bukaci ‘yan Najeriya da suke sauraron sanarwa a kafafen yada labarai kan yadda za a samu wannan tallafin gwamnatin, tare da karin wasu, cikin kwanaki masu zuwa.

Ya kara da cewa hakkin ‘yan Najeriya ne gwamnatin ta gayamusu gaskiya, kuma gwamnati bata sa ran wasu kasashen za su kawo mata dauki domin taimaka mata wajen ganin bayan wannan cutar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − 5 =