Shugaba Buhari Ya Bayar Da Umarnin Raba Tirela 150 Na Shinkafa Da Hukumar Kwastan Ta Kwace

95

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bada umarnin raba shinkafa Tirela 15 a Jihohi 36 wanda hukumar hana fasakwauri ta kasa wato kwastam ta kwace.

Ministan Kudi, kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ita ce ta bayyana haka a lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai a Abuja.

Zan tawa da manema labarai ya biyo bayan kudurin Gwamnatin tarayya na raba tallafi biyo bayan faduwar farashin man fetur da wanda annobar coronavirus ta haifar.

Ministan ta ce Gwamnatin tarayya ta mika Tirelolin shinkafar ga ma’aikatar Jinkai, Iftila’i da cigaban Al’umma domin rabasu ga jihohin kasar nan.

Haka kuma ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da raba kayan abinci wadanda suka hada Gero da Dawa daga wurin da ake ajiye kayan abinci na kasa domin a rabasu ga kasar nan.

Kazalika, ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da rage kudin takin zamani daga N5,500 zuwa N5,000.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × five =