Shugaba Buhari Ya Amince Da Daukar Mutane Dubu 774 ‘Yan Najeriya Aikin Gwamnati Na Musamman A Kasarnan

84

Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, tace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da daukar mutane dubu 774 ‘yan Najeriya, aikin gwamnati na musamman a kasarnan, domin saukaka wahalhalun da annobar coronavirus ta haifar.

Zainab Ahmed ta bayyana haka yayin taron manema labarai akan matakan kare tattalin arziki dangane da illar annobar covid-19 akan farashin danyen mai, wanda aka gudanar a Abuja.

Ta bayyana cewa ana sa ran daukar mutane dubu 1 daga dukkan kananan hukumomi 774 dake fadin kasarnan.

A cewarta, an ware kudi naira biliyan 60 domin biyan alawus-alawus daga kudaden da aka ware domin yaki da annobar covid-19.

Ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari tun a baya ya amince da fara gwajin shirin daukar aikin na musamman a jihoshi 8, karkashin hukumar samar da ayyukan yi ta kasa, NDE.

Ta kara da cewa shugaba Buhari a yanzu ya amince a fadada shirin zuwa dukkan jihoshi 36 tare da babban birnin tarayya, daga watan Oktoba zuwa Disamba na bana, kuma a tabbatar da cewa an fara aiwatar da shi bayan lokacin shuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − two =