Shugaba Buhari A Yau Zai Gana Da Kwamitin Karta Kwana Na Shugaban Kasa Akan Covid-19

46

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau zai gana da kwamitin karta kwana na shugaban kasa akan COVID-19 , dangane da dokar hana fita kwata-kwata da aka kakaba a babban birnin tarayya da jihoshin Lagos da Ogun.

An tattaro cewa kwamitin na karta kwana zai yiwa shugaban kasar bayani akan da halin da ake ciki dangane da yaki da COVID-19, tare da yiwuwar kara wa’adin dokar hana fitar na makonni 2 a babban birnin tarayya da jihoshin Lagos da Ogun, tare da karin wasu sassan kasarnan.

Wasu manyan jami’an gwamnati ne suka tabbatarwa da manema labarai cewa kwamitin na karta kwana zai yiwa shugaban kasar bayani.

Shugaban kasar a jawabinsa da aka watsa a fadin kasarnan ranar 29 ga watan Maris, ya bayar da umarnin hana fita kwata-kwata a a babban birnin tarayya da jihoshin Lagos da Ogun, tsawon makonni 2, farawa daga karfe 11 na daren ranar 30 ga watan Maris.

A cewar shugaban kasa, dokar hana fitar zata bawa gwamnati damar ganowa tare da yin magani ga wadanda suka kamu da kwayar cutar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight − two =