Kimanin Ma’aikatan Lafiya 40 Ne Suka Kamu Da Cutar Corona A Najeriya

17

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire yace kimanin ma’aikatan lafiya 40 ne a Najeriya kawo yanzu suka kamu da cutar corona.

Ehanire ya fadi hakan lokacin da yake jawabi wajen taron bayanin halin da ake ciki na kwamitin karta kwana na shugaban kasa akan COVID-19.

Ya gargadi ma’aikatan lafiya da su tabbatar da daukar matakan kariya lokacin da suke duba duk wani mara lafiya.

Gwamnatin tarayya tunda farko ta hana asibitoci masu zaman kansu karbar masu fama da cutar corona, inda tace dayawa daga cikin ma’aikatan lafiya a asibitocin basu samu horon kulawa da irin wannan cutar ba.

Gwamnatin tarayyar a yanzu ta bukaci asibitocin masu zaman kansu wadanda ke san karbar masu fama da cutar corona da suyi rijista da ma’aikatar lafiya ta jihar da suke, domin tabbatar samun horon ma’aikata yadda ya kamata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven + nine =