Kamfanonin rarraba wutar lantarki sun sanar da cewa suna goyon bayan yunkurin majalisun kasa da bangaren zartarwa na tarayya cewa a bawa ‘yan Najeriya wutar lantarki a kyauta ta watanni 2.
Da suke magana karkashin kungiyarsu, kungiyar masu rarraba wutar lantarki na Najeriya, kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun bayyana cewa ya kamata a samar da tsare-tsaren bayar da wuta kyauta, kuma a bayyanawa jama’a a lokacin da ya dace.
Zababben Daraktan kungiyar, Sunday Oduntan, shine ya bayyana haka cikin wata sanarwar da aka fitar a Abuja.
Ya nanata jajircewar kamfanonin rarraba wutar lantarki wajen inganta ayyukansu a kasarnan, lokacin annobar coronavirus da bayanta.