Gwamnatin Tarayya Za Ta Taimakawa Kano Akan Cutar Corona

24

Gwamantin Tarayya tace ta damu matuka bisa halin da ake ciki dangane da cutar corona a jihar Kano, inda annobar ke yaduwa cikin gaggawa, a cewar jami’an kwamitin karta kwana na shugaban kasa akan COVID-19.

Domin taimakawa jihar, jagora na kasa na kwamitin, Dr. Sam Ajayi, yace ana aikin samar da karin dakin gwaje-gwaje a jihar.

Bayan cutar ta corona, akwai rahotannin yawan mace-mace a jihar, inda aka yi kiyasin cewa mutane 152 aka binne a makabartu daban-daban cikin kwanaki 3 a karshen makon da ya gabata.

Kwamitin karta kwana na shugaban kasa yace zai bincika dalilin mace-macen, wanda gwamnatin jihar ta musanta a baya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − sixteen =