Gwamnan Bauchi Ya Haramta Almajiranci Da Sana’ar Achaba

106

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ya haramta Almajiranci a jihar.

Bala Muhammad a wani jawabi da aka watsa a fadin jihar yace tsohon tsarin almajiranci abu ne wanda aka wuce zamaninsa kuma babu kula da kiwon lafiya a wannan yanayin da ake ciki na annoba cutar corona a jihar.

Gwamnan wanda yace jihoshin Kaduna da Kano suna cikin shirin dawo da Almajirai ‘yan asalin jihar Bauchi zuwa gida, ya kara da cewa gwamnatin jihar ta shirya sansanin horas da matasa masu yiwa kasa hidima a jihar domin ajiye su, kafin daga bisani a sada su da iyalansu.

Bala Muhammad yace Almajiran da suka fito daga wasu jihoshin wadanda ke karatu a jihar Bauchi, suma za a mayar da su zuwa jihoshinsu.

Gwamnan ya kuma haramta sana’ar Achaba, wanda yace sun shigo jihar ta Bauchi daga jihoshi makota.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × one =