Fira-Ministan Birtaniya Ya Fito Bainar Jama’a A Karon Farko Bayan Ya Warke Daga Cutar Corona

49
The Prime Minister Boris Johnson Portrait

Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson, ya fito bainar jama’a a yau, tun bayan da cutar corona ta kwantar da shi a asibiti makonni 3 da suka gabata, inda yace Birtaniya ta fara shawo kan annobar, amma yayi watsi da kiraye-kirayen saukaka dokar kulle a fadin kasar.

Boris Johnson ya rame kuma farin gashinsa ya kara tsayi. A wata sanarwa da aka fitar a ofishinsa domin bayyana komawarsa bakin aiki, Fira-Ministan ya nemi afuwa kasancewar ya dade bai koma aiki ba, fiye da lokacin da yayi tsammani.

Ya godewa mutanen Birtaniya bisa amsa kiran dokar zama a gida, wacce ta taimaka wajen rage bazuwar cutar, duk da kasancewar ta hallaka sama da mutane dubu 20 a kasar. Amma da yake amincewa da damuwar ‘yan kasuwa da dama, da koma bayan tattalin arzikin da ake samu, Boris Johnson yace ba yanzu ne lokacin da za a saukaka dokar kullen ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 4 =