Najeriya Ta Rage Farashin Danyen Manta

61

Najeriya ta rage farashin danyen manta zuwa mafi araha a tarihi, domin samun damar sayar da man a kasuwanni.

Kasarnan na fama da yawaitar mai a kasuwannin duniya, wanda ba a taba gani a baya ba, sanadiyyar cutar coronavirus, da kuma rikicin kasuwanci tsakanin Saudiyya da Rasha.

Farashin gangar danyen mai ta Brent, wacce ake amfani da ita a duniya, ta fadi da sama da kashi 60 cikin 100, tun farkon wannan shekarar. Inda ta kai dala 26 da digo 44 kowace ganga, da misalin karfe 7 da minti 40 na yammacin jiya Litinin.

Shugaban kamfanin mai na kasa, NNPC, Mallam Mele Kyari, ya fada a ‘yan kwanakinnan cewa kasar na shan wahalar samun masu sayen danyen man ta, inda yace sama da jiragen ruwan danyen mai 50 ne ba a samu saye ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen + six =