Mansur Manu Soro Yayi Rabon Kabakin Arziki Ga Mutanen Mazabarsa

411

Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Darazo da Ganjuwa a jihar Bauchi, Honorable Mansur Manu Soro, ya kaddamar da kashin farko na rabon tallafin kayayyakin sana’o’i da na more rayuwa, wanda aka gudanar a cikin garin Bauchi.

Wannan mataki ne daga cikin manyan kudirorinsa na kokarin rage radadin fatara da talauci tsakanin jama’arsa, duba da halin da al’ummar yankin Arewa maso Gabas na kasarnan ke ciki na rashin ayyukan kai, tare da rashin mayar da hankali kan sana’o’i.

Yayin kaddamar da rabon, Mansur Manu Soro, wanda ya samu wakilcin hadiminsa, ya shawarci wadanda suka amfana da tallafin, da suyi kakykyawan amfani da kayayyakin ta hanyar da ta dace.

A nasa jawabin, jagoran kwamitin rabon kayayyakin, Honorable Sai’du Isah Abdu, ya sanar da cewa wannan rabon shine kashin farko, kasancewar za a gudanar da wani rabon a kashi na biyu, nan ba da dadewa ba.

Daga nan cikin wadanda suka halarci rabon, sun hada da shugabannin jam’iyyar APC na karamar hukumar Darazo da na karamar hukumar Ganjuwa.

Daga cikin kayayyakin da aka raba sun hada da babura da injinan nika da injinan wuta da kayan wutar lantarki na hasken rana, solar, da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + 11 =