Hukumar Tara Kudaden Shiga Ta Kasa FIRS Ta Yiwa Manyan Daraktoci Ritaya

25

Kwamitin gudanarwa na hukumar tara kudaden shiga ta kasa ya amince da ritayar dukkan daraktocin hukumar wadanda suka yi aiki tsawon shekaru 8.

Kwamitin ya kuma amince da nadin daraktocin rikon kwarya guda 4 da wasu shugabannin rikon kwarya guda 2.

Daraktan sadarwa da sashen hulda da jama’a na hukumar, Abdullahi Ahmad, shine ya tabbatar da hakan a Abuja.

Yace matakin yana daga cikin sauye-sauyen da ake yi a hukumar domin yi mata garanbawul wajen samun nasarar cimma tara harajin kudi naira tiriliyan 8 da biliyan 500, da ake sa rai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 + 16 =