Hukumar Kwastan Tayi Karin Girma Ga Kananan Jami’anta Guda 2,974

109
Kanar Hameed Ali mai ritaya, shugaban hukumar hana fasa-kwauri

Shugaban Hukumar Hana Fasa Kwauri, Kwastan, Kanal Hamid Ali, mai ritaya, ya amince da karin girma ga kananan jami’an hukumar su 2,974 zuwa matsayi daban-daban.

An tabbatar da karin girman a cikin wata sanarwar da kakakin hukumar, Joseph Attah, ya fitar.

Sanarwar tace an yi karin girman bisa cancanta kadai.

Ta kuma ce yayin karin girman, anyi la’akari da makin auna kokarin jami’an, da na jarabawar da suka zana da kuma matsayinsu tare da samun gurabe a matsayin gaba da za a kai su.

Da yake bayar da amincewarsa domin karin girman, shugaban hukumar ta kwastan, ya taya murna ga dukkan jami’an da aka yiwa karin girman, tare da bayyana fatan cewa karin girman zai zama abinda zai karfafa musu gwiwa domin kara himma wajen gudanar da ayyukansu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − 4 =