Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci ‘Yan Najeriya Da Su Shirya Fuskantar Tsauraran Matakan Dakile Coronavirus

24

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Najeriya da su shirya fuskantar tsauraran matakan dakile cigaban yaduwar cutar coronavirus da ake fama da ita.

Gwamnatin tace za a sanar da matakan nan da awanni 24 zuwa 48.

Gwamnatin tace zata iya fara amfani da sojoji da ‘yansandan Najeriya wajen gano wadanda suka yi mu’amala da wani mai dauke da cutar.

Ta bayyana damuwar cewa sama da mutane 1,300 wadanda suka yi mu’amala da wasu masu cutar, sun bace cikin jama’a, kuma har yanzu ba a gano su ba.

Gwamnatin tace bisa la’akari da yiwuwar rubanyar yawan wadanda suka kamu da cutar cikin kwanaki 5, dubban mutane zasu iya kamuwa.

Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, shine ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a Abuja.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 1 =